A wannan rana, sakatare janar na M.D.D. Ban ki-moon ya yi jawabi, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da kudin tallafi wajen yaki da cutar, da sa kulawa sosai ga wadanda suke fama da cutar, da taimakawa wajen gano sabbin hanyoyin yaki da cutar. Ban da wannan kuma, Ban ki-moon ya yi nuni cewa, yanzu, kasashen duniya na nuna jinkiri ga kara ba da tallafin kudi sosai wajen yaki da cutar, dalilin haka ne, ake samun tafiyar hawainiya wajen daukar matakan yaki da cutar, da rarraba gidajen sauro. Haka kuma, ya bukaci hukumomin kiwon lafiya na kasashen duniya, cikinsu har da gwamnatocin kasashen da ke fama da cutar zazzabin cizon sauro da su cika alkawarin da suka dauka wajen kara samun hanyoyin rigakafin cutar, ta yadda, za a kawo karshen wahalar da masu fama da cutar suke sha.(Bako)