in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke wani jagoran masu garkuwa da mutane a Najeriya
2013-09-26 15:24:12 cri

Jami'an tsaron farin kaya a tarayyar Najeriya sun bayyana cafke wani mai suna Kelvin Obvrubie, bisa zarginsa da jagorantar laifuka masu alaka da yin garkuwa da mutane, musamman a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir a kasar.

Jami'an hukumar tsaro ta SSS sun ce, sun samu nasarar damke Obvrubie, tare da wasu mutane 4, a ranar 17 ga watan nan ne a wani daji dake yankin Osubi, a jihar Delta.

Da take karin haske kan wannan batu a Asaba, babban birnin jihar ta Delta, daraktar hukumar ta SSS a jihar Florence Ikanon, ta bayyanawa manema labarai cewa, wanda ake zargin na cikin jerin gungun masu laifi da ake nema ruwa a jallo. Ta ce, baya ga zargin jagorantar 'yan fashi da makami a lokuta daban daban, Obvrubie ya yi ikirarin kasancewa cikin wadanda suka yi garkuwa da mutane da dama, ciki hadda wani mai suna Rufus Uzoma, ma'aikaci a matatar man fetir dake garin Warri, a ranar 10 ga watan Agustan da ya gabata.

Ikanon, ta kuma ce, yanzu haka jami'an hukumar na dada kaimin zakulo ragowar bata garin da ke cikin gungun masu laifin, yayin da a hannu guda ta alkawarta gurfanar da wadanda aka riga aka cafke gaban kuliya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China