Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya ce, wata tawagar musamman ta masu bincike kan makamai masu guba na daf da tashi zuwa kasar Sham, a shirin da ake yi na gudanar da aikin tantance yiwuwar amfani da makamai masu gubar a lokutan da ake tsaka da dauki-ba-dadi a kasar.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar ranar Laraba 14 ga wata, Mr. Ban ya ce, tawagar kwararrun ta MDD mai kunshe da mutane 10, wadda aka kaddamar a birnin Hague tun a farkon wannan wata na Agusta, ta samu cikakkiyar amincewar gudanar da sahihin aiki daga mahukuntan kasar ta Sham.
Da yake bayyana farin cikinsa don gane da shirin gudanar da bincike kan aukuwar wannan lamari, Ban ya ce, burin MDD shi ne, aiwatar da sahihin bincike bisa adalci. Ya ce, ya yi imanin tawagar da aka dorawa alhakin gudanar da wannan aiki, cike take da kwararru, kuma masana makaman aiki. Har ila yau, Ban ya yaba wa hukumar yaki da amfani da makamai masu guba, da hukumar lafiya ta WHO, bisa muhimmin goyon baya da suka baiwa wannan shiri.
Ana dai sa ran tawagar kwararrun za ta shafe a kalla makwanni biyu tana gudanar da ayyukanta, wadanda za su hada da ziyartar wurare irinsu Khan Al-Asal, wanda daya ne daga wuraren da ake zargin an yi amfani da irin wadannan makamai masu guba.
Kimanin mutane 25 ne dai aka tabbatar da rasuwarsu, baya ga wasu 130 da suka jikkata, sakamakon harba wata roka mai dauke da sanadarai masu guba da wasu mahara suka yi, a ranar 19 ga watan Maris din da ya gabata, laifin da bangarorin mahukuntan kasar da na 'yan adawa suka musanta aikatawa. (Saminu)