in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Chadi ta bayyana takararta ta neman kujera a kwamitin sulhun MDD
2013-09-26 13:09:12 cri

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya bayyana a ranar Laraba a yayin mahawara a babban taron MDD takarar kasarsa a kwamitin sulhu na MDD, a cewar wata sanarwa da MDD ta fitar bisa shafinta na internet. Wannan makoma ta tushe ita ce babbar niyya ta gabatar da takararmu bisa kujerar zaman mamba na wucin gadi a kwamitin sulhu na MDD bisa wa'adin shekarar 2014 zuwa ta 2015, in ji shugaban kasar Chadi, tare da tunatar da cewa, kasarsa ta taba tura yawan sojoji fiye da 2000 a kasar Mali, sannan akalla sojoji 900 a kasar Afrika ta Tsakiya.

A cewar shugaba Deby, kusan sojojin kasar Chadi 1800 za su shiga cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke kasar Mali (MINUSMA).

Haka kuma Chadi ta tura sojojinta a cikin ayyukan samar da zaman lafiya na MDD a kasashen Cote d'Ivoire, RDC-Congo da kuma kasar Haiti.

Game da kasar Afrika ta Tsakiya, mista Deby ya yi kira ga kwamitin sulhun da ya cimma wata hanya mai kyau da za ta taimaka ga cimma hanyoyin samun taimakon kudi da kayayyaki ga tawagar MDD ta MISCA. Kuma ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta cigaba da samar da taimakon jin kai ga 'yan gudun hijira na yankin Darfur a yayin da tashe-tashen hankali na siyasa da kabilanci ke dada karuwa. Mafita mai karko kuma ta din din din ga dukkan wadannan tashe-tashen hankali dake mai da hannun agogo baya ga cigaban Afrika ita ce yaki da talauci, ci da gumin mutane da kuma rashin aikin yi na matasa, in ji shugaban kasar Chadi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China