An nada tsohon ministan noma na kasar Chadi, dokta Djimet Adoum a matsayin sakatare zartaswa na kwamitin din din din na kasashen dake yaki da fari da gusowar hamada a yakin Sahel (CILSS), a cewar wata sanarwar karshen taro a ranar Lahadi, wadda ta cike taro karo na 16 na wannan kungiya da ya gudana a ranar Asabar a birnin N'Djamena na kasar Chadi.
Haduwar ba ta samu halartar tawagogin kasashe da dama ba, shugaban kasar Mali Dioncounda Traore kadai ne bisa matsayin shugaban kasar da ya halarci wannan taro na N'Djamena a yayin da kasashen Cote d'Ivoire da Burkina Faso suka aika faraministocinsu, sannan sauran kasashe mambobin kungiyar suka aika da ministocinsu.(Maman Ada)