A ranar Alhamis, kasar Chadi ta bayyana cewa, yunkurin juyin mulki barazana ce ga dorewar cibiyoyin demokradiyya a jamhuriyar.
'Gwamnatin kasar Chadi a ranar Laraba ta murkushe wani yunkuri na abin da ta kira 'wani gungun mutane masu muguwar aniya.' in ji Hassan Sylla ben Bakary, mai magana da yawun ma'aikatar sadarwa, ya bayyana wa gidan talbijin din kasar ranar Alhamis.
Ya ce, masu makarkashiyar sun shafe sama da watanni hudu suna kulla makircin kawo baraka ga zaman lafiya karkashin shugabancin Idriss Deby Itno.
Mahukunta a kasar sun cafke manyan sojoji da ma wasu jami'an soji da fararen hula, ciki har da wani 'dan majalisa, a safiyar ranar Alhamis.
Jami'an tsaro sun shiga wani aikin yaki da masu shirya juyin mulkin a bayan garin N'Djamena a ranar Laraba, inda aka samu harbe-harben bindiga, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, kana sama da mutane 12 sun samu rauni, in ji 'yan sanda.(Lami)