in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aurar da kananan yara na kawo cikas ga shirin muradun karni a Ghana
2013-08-27 12:45:57 cri

A kasar Ghana, aurar da kananan yara na kawo cikas ga shirin muradun karni na MDD, kamar yadda alkaluma suka nuna cewa, ana aurar da yara mata kafin su cika shekaru 18 wanda shi ne kayyadaden lokacin isa aure na MDD.

Ministan jinsi, yara da kariyar zamantakewa Nana Oye Lithur wadda ta yi gargadin game da sakamakon hakan a ranar Litinin, ta ce, idan ba'a daina aurar da 'ya'ya mata da wuri ba, to hakan zai haifar da kasa cimma muradu 4 daga cikin 15 wato, samar da ilimi firamare ga kowane yaro, inganta daidaito na jinsi duka, rage mutuwar jarirai bayan an haife su, da kuma, inganta lafiyar mai juna biyu.

Madam Nana Lithur ta ce, dokar hana cin zarafin mata a cikin gidajensu ta shekarar 2007, dokar hana fataucin mutane ta shekarar 2005, da kuma kafa dokar kula da wadanda aka ci masu zarafi a gida da sashin taimaka masu na rundunar 'yan sandan kasar Ghana, duk an fitar da su ne domin tabbatar da 'yancin yara a kasar.

A cewar ta, auren wuri ga kananan yara yana haifar tare da yada talauci ya kuma kara yawan dogaro a kan wassu da kuma kara yawan marasa ilimi, musammam ma a cikin jinsin mata, inda ta yi bayanin cewa, hakan na kara ingiza mata shiga haddura na rayuwa da rashin tabbas da ya jibanci cin zarafi har a cikin gidajensu.

Shi ma a nashi tsokacin, mataimakin ministan yada labarai Murtala Mohammed ya lura cewa, bukatun dake cikin aurar da yara kanana da yawan hayayyafa a zaman da ya sha banban da wannan zamani da muke ciki, don haka ya kamata a lura da banbanci a daina yinsa.

Dokar kasar ta amince da cewa, sai 'yar mace ta cika shekaru 16 ne za ta amince ko ta sadu da namiji ko kuwa a'a, amma aure kuma sai ta cika shekaru 18 da haihuwa.

Kasar Ghana dai ta bi sahun sauran kasashen duniya ne wajen bikin ranar yara a ranar 27 ga wata karkashin taken "hana auren wuri, nauyi ne a wuyanmu gaba daya." (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China