in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mugabe ya yi gargadin hukunta kamfanonin kasashen yamma don nuna takaicinsa kan takunkumin shekaru 10
2013-08-26 10:23:34 cri

Shugaba Robert Mogabe na Zimbabwe a ranar Lahadin nan 25 ga wata, ya sanar da cewa, zai yi ramuwar gayya a kan takunkumin da kasashen yamma suka saka na fiye da shekaru 10 a kan kamfanonin wadannan kasashen dake huldar kasuwanci a kasar, idan dai har kasashen Ingila da Amurka suka cigaba da tsoma baki a cikin harkokin kasarsa.

Shugaban wanda ya isar da wannan gargadin da kakkausar murya a wajen jana'izar wannan mai fada a ji na jami'iyyarsa ta ZANU-PF Mike Karakadzai, ya ce, kasar za ta dauki mataki mai tsanani a kan kamfanonin kasashen Amurka da Ingila dake aiki a kasarsa idan dai har kasashen suka cigaba da sa ma shi ido.

Tun dai a shekara ta 2010, jami'yyar dake mulki a kasar ta Zimbabwe ke ta kokarin ingiza wani tsari na tattalin arzikin wanda ya bukaci ko wane kamfanin kasar waje ya hakura da kashi 51 a cikin 100 ga 'yan kasa, tsarin da ya fara da kamfanonin ma'adinai da bankunan kasashen waje.

Shugaba Mugaba wanda ya ce kasarsa ta yi dauriya iyakar dauriya game da takunkumin da kasashen wajen suka kakaba ma kasarsa, don haka ba zai taba neman ra'ayin wadannan kasashen ba komin rintsi, ya kuma soki abokin hamayyarsa Morgan Tsvangirai wanda yana bauta ma Turawa suna ba shi gurguwar shawara, wadda daga cikinsu ita ce, bukatar da ya gabatar da yin kwaskwarima ga tsarin tsaron kafin babban zaben da aka kammala a kasar,

Mugaba har ila yau ya yi tir da halayyar mazauna Harare, babban birnin kasar da kuma Bulawayo, birni mafi girma na biyu, a dalilin kuri'unsu gaba daya da suka jefa ma jam'iyyar adawa, abin da ya bata nasarar lashe kuri'un 'yan majalissar dokoki na wadannan wurare, sannan ya soki wanda da ke da ra'ayin hana tsoffin jami'an soji rike wani mukami a ko wace ma'aikata ta gwamnati. Shi dai marigayi Mike Karakadzai wanda kafin rasuwarsa tsohon shugaban hukumar kula da zirga zirgan jiragen kasa ne, sannan tsohon hafsan sojin sama a rundunar sojin kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China