A ranar Talatan nan 10, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sanar da sunayen sabbin 'yan majalissar zartarwarsa da zai yi aiki da su na tsawon shekaru biyar.
Shugaba Mugabe dai ya samu kashi 61 cikin 100 na kuri'un da aka jefa lokacin babban zaben kasar, abin da ya ba shi nasasar zarcewa da shugabancin kasar, abokin hamayyarsa, Morgan Tsvangirai wanda shi ne tsohon firaministan kasar ya samu kashi 34 a cikin 100.
Jam'iyyar dake mulki ZANU-PF har ila yau ita ke da rinjaye da kashi biyu cikin uku na kujeru a majalissar dokokin kasar.
Sabuwar gwamnatin da aka kafa ta kawo karshen gwamnatin Hadaka tsakanin jam'iyyun adawa MDC-T da MDC-M da mai ci yanzu ZANU-PF wanda aka kafa a shekara ta 2009 sakamakon tashe-tashen hankula da kasar ta fuskanta shekara guda kafin wancan babban zaben. (Fatimah)