Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe ya ce, dukkanin wani takunkumi da kasashen yamma za su kakabawa kasarsa, ba zai gurgunta manufar da ya sanya a gaba, ta samar da ci gaba ga al'umma ba, ciki hadda manufofinsa na bunkasa tattalin arziki, da samar da ababen more rayuwa, da inganta harkokin sufuri da dai sauransu.
Shugaba Mugabe ya bayyana hakan ne ranar Laraba 11 ga watan nan, yayin wani taron manema labarai da ya gudanar, jim kadan da rantsar da sabbin 'yan majalissar zartaswar kasar.
Ya ce, za su yi cikakken amfani da ma'adinai da albarkatun kasar, da hadin kan kasashe masu yiwa kasar tasa kyakkyawan fata, wajen ciyar da ita gaba. Ko da yake dai jam'iyyarsa ta Zanu-PF ta dade da bayyana cewa, takunkumin da aka kakabawa kasar ya haifarwa tattalin arzikinta asarar biliyoyin daloli.
Wannan tsokaci dai na Mugabe na zuwa ne daidai lokacin da kasashen Birtaniya da Amurka ke ci gaba da aiwatar da takunkumin da suka kakabawa kasar tun cikin shekara ta 2000, A baya-bayan nan kuma suka bayyana cewa, ba za su janye takunkumin ba, sakamakon zargin tafka magudi da suka ce an yi yayin babban zaben kasar na ran 31 ga watan Yulin da ya gabata, wanda aka bayyana cewa, jam'iyyar shugaba Mugaben ta Zanu-PF ta lashe.
Bugu da kari Mugabe ya bayyana cewa, zai ci gaba da gudanar da dukkanin manufofinsa na mai da kadarori hannun 'yan kasa, tsarin da ya tanaji dukkanin kamfanonin waje dake kasar ala tilas su mika kaso da bai gaza 51 bisa dari na hannayen jarinsu ga 'yan kasa.
Har ila yau shugaban kasar ta Zimbabwe ya ce, ko da yake abu ne mai kyau a gudanar da gwamnati tare da 'yan adawa, a hannu guda mawuyaci ne ya iya aiki tare da su sakamakon irin halayyar da suke nunawa ta rashin kishin kasa. (Saminu)