in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 17 suka mutu a arangama tsakaninsu da Boko Haram a Nijeriya
2013-09-09 10:26:37 cri

A jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya, akalla mutane 17 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani arangama da suka yi tsakaninsu da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram a safiyar ranar Lahadin nan da ta gabata.

Kamar yadda mazauna Benisheik, unguwar da hakan ya faru suka tabbatar wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua, sun ce, hakan ya faru ne lokacin da 'ya'yan kungiyar suka far ma 'yan banga wadanda aka kashe 12 daga cikinsu, har ila yau su ma 'yan banga suka samu nasasar kashe 5 daga cikin 'yan Boko Haram din, abin da ya zama fito na fito mai tsanani, in ji malam Yusuf Bello, wani mazauni da ya gane ma idanunsa.

Haka shi ma daya daga cikin 'yan banga dake kwance a sashin kula da masu hadarin gaggawa na asibitin koyarwa na jami'an Maiduguri, Zannah Fannami ya tabbatar da wannan al'amari da ya kira abin bakin ciki inda abokan aikinsa 12 suka rasu.

Yanzu haka dai an girke jami'an tsaro na soji a wannan unguwa kuma an samu nasarar kawo karshin harin, in ji Sagir Musa, kakakin rundunar tsaro ta hadin gwiwwa a jihar.

Wannan hari ya faru ne kwanaki biyar da sojoji suka dakile hare-hare har sau biyu a kauyukan Gajiram da Bulablin inda a nan ma aka kashe mutane 15 su kuma rundunar tsaro a ranar Juma'a da ta gabata suka tabbatar da nasarar kashe akalla mutane 50 daga cikin 'ya'yan kungiyar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China