in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jami'in diplomasiyyar Amurka ya ba da hujjar fitar da Najeriya daga gasar walawalar visa ta shekarar 2015
2013-09-21 16:37:22 cri
Wani jami'in diplomasiyyar Amurka ya ba da hujjar da kasarsa ta dauka ta tsai da kasar Najeriya daga tsarin gasar walawalar takardar visa ta shekarar 2015.

Tsarin da gwamnatin Amurka take amfani da shi wajen shigo da mutane daga kasashen da ba su da wakilci sosai a kasar Amurka.

Aya mai lamba 203 ta doka kan baki da takardar kasa (INA) ta kasar Amurka na kebe a kalla visa dubu hamsin da biyar a ko wace shekara domin bai wa mutanen dake fitowa daga kasashen da ba su da yawan mutanensu a kasar Amurka.

Takardun na visa ana rarraba su zuwa yankuna kashi shida, inda yawancinsu ake bai wa kasashen da mutanensu ba su shiga kasar Amurka da dama, kana bai wa kasashen dake turo fiye da mutane dubu 50 zuwa kasar Amurka a tsawon shekaru biyar na baya-bayan nan ba.

Kasa guda ba za ta iyar samun fiye da kashi 7 cikin 100 na wannan takardar visa ba cikin shekara guda ba. Tare da kasar Najeriya da ta cimma adadi na fiye da mutane dubu hamsin, kasar ke nan ba ta da damar ci gaba da samun wannan alfarmar wannan tsari ba, in ji karamin jakadan kasar Amurka Jeffrey Hawkins a ranar Alhamis a birnin Lagos. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China