Sojojin sun ce, sun kai samamen ne kan wani gida da suke zargin maboyar 'yan kungiyar nan ne ta Boko Haram, lamarin da ya janyo musayar wuta, aka kuma harbe 'yan bindigar 14, tare da soja guda daya.
Mazauna wannan yanki na Unguwa Uku dake birnin Kano sun ce sun ji karar harbe-harbe da kuma fashewar abubuwa, lamarin da ya sanya su buya cikin gidajensu kafin lafawar dauki ba dadin.
A wata sabuwa kuma, jami'an tsaron na JTF, sun murkushe wani yunkuri na kai harin kunar-bakin-wake a wannan rana a garin na Kano, tare da kwace wasu bindigogi guda 14 kirar AK-47 daga hannun 'yan bindiga.
Ana dai sha fama da tashe-tashen hankali a yankunan arewacin Najeriya tun daga shekara ta 2010, tare da aukuwar hare-haren kunar-bakin-wake a wasu wuraren taruwar jama'a da wuraren ibada, matakinda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu 1.
A yunkurinsu na murkushe 'yan kungiyar nan ta Boko Haram, wadda ake dorawa alhakin yawancin hare-haren dake wakana a wannan yanki, rundunar sojojin gwamnatin Najeriya sun sha kai samame na ba-zata, a wuraren da ake zaton mabuyar 'yan kungiyarce. (Murtala)