in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Angola za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa na duniya na matasa `yan kasa da shekaru 20
2011-08-26 15:02:36 cri

A wani bangare na bikin taya murnar cika shekaru 69 na shugaba Jose Eduardo dos Santos na kasar Angola,lardin Cabinda mai arzikin man fetur dake kasar zai karbi kakuncin gasar wasan kwallon kafa na duniya na `yan kasa da shekaru 20 wanda za a gudanar daga ranar 25-28 na wannan watan.

Ana sa ran gudanar da gasar a filin wasa na Chiazi dake Cabinda kuma kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Angola, Janhurriyar demokradiyyar Congo, Gabon, da Congo brazaville ne za su fafata a tsakanin su domin taya wannan shugaba murna da zai cika shekaru 69 a ranar 28 ga wannan watan na Augusta.

Shi dai yankin Cabinda yana wani ziri ne daya ratsa ta kasar DR congo, kuma lardin yana daya daga cikin wuraren da aka hakar mai a duniya.(bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China