Dos Santos wanda ya bayyana hakan a jawabin sa na shekara shekara ranar 18 ga wata ya ce, kasar Angola tana bin ka'idar warware rikice-rikice a duniya ta hanyar yin shawarwari, kuma tana adawa da warware batutuwan duniya ta hanyar nuna karfin tuwo.
Shugaban ya jaddada cewa, kasar Angola za ta ci gaba da tsayawa kan kiyaye mulkin kai da cikakken yankin kasar, kuma tana adawa da kasashen waje da suke sa hannu cikin harkokin cikin gidanta.
Ya ce kasar Angola za ta ci gaba da daukan nauyinta, da ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen yaki da 'yan ta'adda da haramtar da kazamin kudi da sayar da miyagun kwayoyi ta hanyar sumogal da sauransu.(Abubakar)