A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, yanayin Beijing ba shi da inganci kamar yadda ya kamata, wato an yi hazo mai tsanani, hakan ya sa ma'aunin ingancin iska da ake aiwatarwa a cikin 'yan shekarun da suka wuce ya jawo hankalin jama'a, game da wannan, a ran 21 ga wata, ministan ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar Sin Zhou Shengxian ya nuna a Beijing cewa, kasar Sin tana yin kokari matuka domin tsara sabon ma'aunin ingancin iska cikin gajeren lokaci. A shekara mai zuwa, wasu muhimman wurare kamar su Beijing da Shanghai za su tsara sabon ma'aunin wanda zai kai na kasa da kasa a kai a kai, da haka, ana fatan sakamakon binciken da za a samu zai yi daidai da yadda jama'ar kasa ke ji ko gani. Wannan aiki shi ne daya daga cikin ayyukan da kasar Sin ke yi domin sa kaimi kan aikin rage gurbatar muhalli da tsimin makamashi.
A yayin taron tattaunawa kan aikin kiyaye muhalli na duk kasar Sin da aka yi a wannan rana, Zhou Shengxian ya jaddada cewa, kyautata ingancin muhalli zai amfanawa aikin kiyaye muhalli, shi ya sa, ya kamata a bayyana bukatun jama'ar kasa ta hanyar tsara ma'aunin ingancin muhallin yadda ya dace. Zhou Shengxian ya ce, "Ya kamata a kara kyautata ma'aunin ingancin muhalli kamar na iska da na ruwa da na gonaki da sauransu, kuma ya kamata a samu sakamakon binciken da zai yi daidai da yadda jama'a ke ji ko gani, ban da wannan kuma, dole ne aikin kiyaye muhalli ya bayyana fatan alheri da bukatu na jama'a, da haka, jama'ar kasa za su yi kokari tare domin kara kiyaye muhalli."
A kasar Sin, batun da ya shafi muhalli ya riga ya yi tasiri ga zaman rayuwar jama'a, wani lokaci kuwa, al'amarin kazantar da muhalli mai tsanani ya kan faru. A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, an yi hazo mai tsanani a birnin Beijing, mazaunan birnin sun fara mai da hankali kan wasu kalmomin sana'a wajen kiyaye muhalli kamar PM 2.5, shi ya sa suka nuna shakku kan ma'aunin binciken ingancin muhallin da kasar Sin ke aiwatarwa a halin yanzu.
Kan wannan batu, Zhou Shengxian, a ganinsa, hakan zai ba da gudummawa wajen ciyar da sha'anin kiyaye muhalli gaba, kuma ya nuna cewa, za a yi kokari domin gyara da kuma kyautata ma'aunin. Ya ce, "A wurare daban daban na kasar Sin, akwai bambanci da dama a fannonin alamar kazantarwar iska da matsayin bunkasuwar tattalin arziki da bukatun tafiyar da harkokin kiyaye muhalli da sauransu. Saboda haka, ana shirin yin aikin share fage da yawa kafin a tsara sabon ma'auni. Yanzu muna yin kokari matuka saboda aikin kiyaye muhalli yana da muhimmanci kwarai."
Bisa shirin shekara shekara da ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar Sin ta tsara, an ce, a shekarar 2012, za a fara yin bincike kan wasu abubuwan dake cikin iska kamarsu PM 2.5 da O3 a wasu manyan birane kamar su Beijing da Shanghai da Guangzhou, a shekarar 2013, za a yi wannan aiki a birane sama da dari daya, ya zuwa ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2016, za a fara gudanar da sabon ma'aunin a duk kasar Sin, kuma za a sanar da sakamakon binciken da za a samu ga jama'ar kasa.
A cikin rahoton aiki na shekarar 2012 da Zhou Shengxian ya gabatar, ya yi bayani cewa, a wuraren da suka fi fama da matsalar gurbatar muhalli, ya kamata a kayyaden yawan kayayyakin da suke gurbatar muhalli misali mota da sauransu domin rage gurbatar muhalli tare da tsimin makamashi. Zhou Shengxian ya ce, "Ya kamata a nuna kwazo da himma kan aikin kara amfani da makamashi mai tsabta, kuma a yi kokarin kayyaden yawan iska mai gurbatar muhallin da wasu sana'a'i kamarsu wutar lantarki da karfe da man fetur suke fitarwa. A sa'i daya kuma, a yi kokarin shawo kan gurbatacen iska da motocin ke kawo wa muhalli."(Jamila)