Kwanan baya, an yi taron kara wa juna sani kan ingancin iska na kasa da kasa a karo na 7 a birnin Beijing, a yayin taron da aka yi, mataimakin ministan ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar Sin Zhang Lijun ya nuna cewa, a cikin shekaru 5 masu zuwa wato daga shekara ta 2011 zuwa ta 2015, Sin za ta yi kokarin daukar matakai domin rage da kuma kayyaden fitar da gurbataciyar iska iri daban daban, yanzu ga cikakken bayanin da wakilinmu ya aiko mana.
A cikin shekaru 5 da suka gabata, kasar Sin ta samu babban sakamako kan aikin rage fitar da gurbataciyar iska. Misali, kwatankwacin yawan iskar SO2 wato gurbataciyar iska mafi tsanani da aka fitar a shekarar 2010 ya ragu bisa babban mataki in an kwatanta shi da na shekarar 2005 har ya kai kashi 14.29 cikin dari. Ba ma kawai kasar Sin nuna kwazo da himma kan aikin ingiza tsabtatacen makamashi a birane ba, har ma ta daina yin amfani da wasu kayayyakin konar kwal masu samar da dumamar daki a yanayin sanyi. Ban da wannan kuma, Sin ta tsara wani sabon tsari game da aikin tabbatar da ingancin iska a wasu yankuna a yayin da aka shirya gasar wasannin Olympic a birnin Beijing da bikin baje kolin duniya a birnin Shanghai da gasar wasannin Olympic ta Asiya a Guangzhou. Kazalika, kasar Sin tana aiwatar da manufar "musayar sabuwar mota da tsohuwarta", a sakamakon haka, gaba daya, a duk fadin kasar Sin, an daina yin amfani da tsoffin motoci da yawansu ya kai dubu dari biyu da tamanin da takwas kafin lokacin da aka tanada, a sa'i daya kuma, yawan kayayyki masu gurbata muhalli da aka rage fitar da su a ko wace shekara ya kai ton wajen dubu dari biyu da goma.
Kan wannan batu, Zhang Lijun ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, ingancin iska a kasar Sin ya samu kyuatata a bayyane, amma yanayin muhallin iska na Sin ya yi tsanani sosai, wato gurbataciyar iskar da aka fitar ta yi yawan gaske, har ta kawo babban tasiri ga zaman rayuwar jama'a, kuma ingancin muhallin iska a birane shi ma bai biya bukatun jama'a ba. Zhang Lijun ya ce, "Na farko, a shekarar 2010, yawan gurbataciyar iskar SO2 da aka fitar a kasar Sin ya kai ton miliyan 22 da dubu dari shida da saba'in da takwas, wato ya fi yawa a duniya. har ya sa kasar Sin ta gamu da matsala a wannan fanni. Na biyu, ingancin muhallin iska na biranen Sin ba shi da kyau, kuma ma'aunin ingancin iskar muhalli na Sin bai kai matsayi na kungiyar kiwon lafiyar duniya ba. Shi ya sa, ana iya cewa, yawancin biranen Sin wadanda suka kai ma'aunin inganci na matsayi na Sin ba su kai na kungiyar kiwon lafiyar duniya ba."
Zhang Lijun ya ci gaba da cewa, shekaru 5 masu zuwa lokaci ne mafi muhimmanci ga kasar Sin yayin da take kokarin ginuwar zamantakewar al'umma na samun isashen abinci da sutura, masana'antu da garuruwa za su ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata, kuma yawan kwal da motoci da za a yi amfani da su zai su kara karuwa cikin karancin lokaci, saboda haka, aikin magance da kuma shawo kan gurbatar iska zai gamu da matsala mai tsanani. Game da wannan, kasar Sin za ta dauki jerin matakai domin kara karfafa karfinta kan wannan. Zhang Lijun ya nuna cewa, "Za a kara kyautata aikin samar da ruwa da lantarki da bakin karfe da sauransu wadanda suka fi samar da gurbataciyar iska. Ban da wannan kuma, ya kamata a kara kyautata tsarin sha'anonin da abin ya shafa wato a kara karfafa aikin amfani da makamashi mai tsabta. Kuma ana yin kokarin rage gurbatar iska da hayakin ababen hawa ke fitarwa."
Zhang Lijun ya ce, a cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta kara zuba jari kan aikin magance da kuma shawo kan gurbatar iska da za a fita, kuma za ta ingiza aikin kwaskarima kan harajin muhalli, ana fatan za a daga matsayin kyautata ingancin iska a kasar Sin daga duk fannoni ta hanyar daukar matakai a jere. A karshe dai, ana fatan za a cimma burin rage yawan gurbatar iska iri ta SO2 a shekarar 2015 har zai kai kashi 8 cikin dari in an kwatanta shi da na shekarar 2010.(Jamila)