130913-kasar-Sin-za-ta-yaki-da-gurbatacciyar-iska-Bako.m4a
|
A ranar 12 ga wata, gwamnatin Sin ta bayar da wani shiri na yaki da gurbatacciyar iska, a kokarinta na sassauta gurbacewar iska. A cikin shirin, an bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2017, za a rage yawan kananan sinadaran da ke cikin iska da kashi 10% a birane da garuruwan kasar Sin, haka kuma, za a kokarta don kawar da gurbacewar iska cikin shekaru 5 ko fiye.
Shirin yaki da gurbatacewar iska ya gabatar da matakai guda 35 da za a dauka, wadanda suka shafi daidaita tsarin yin amfani da makamashi, da kayyade yin amfani da motoci, da canja salon raya sana'o'i, da matakan da za a dauka a yayin wani al'amari na ba zata, da sauran fannoni 10, wadanda kuma suka nuna cewa, gwamnatin Sin tana kokarin daukar jerin matakan a fannoni daban daban don warware batun gurbatacewar iska.
Bisa ga shirin, ya zuwa shekarar 2017, za a rage yawan kananan sinadaran da ke cikin iska da kashi 10 cikin 100 a manyan birane da garuruwan kasar bisa na na shekarar 2012, kuma a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, za a kayyade yawan kananan sinadaran da ke cikin iska da yawansu ya yi kasa da microgram 60 a cubia mita guda.
Game da wannan, mataimakin shugaban kwalejin nazarin harkokin kiyaye muhalli na jami'ar Renmin ta kasar Sin Zou Ji ya bayyana cewa, wannan ya zama wani babban aiki ga birnin Beijing, yana mai cewa, "Idan birnin Beijing ya cimma wannan buri, wato kayyade yawan kananan sinadaran da ke cikin iska ya yi kasa da microgram 60 a cubic mita, wato zai kai ga ma'aunin da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta tsara wa kasashe masu tasowa a fannin ingancin iska. ma'ainin da ya kai ga kasa da microgram 30 a kasar Amurka, sai dai don yin la'akari da halin da kasashe masu tasowa ke ciki, wadanda suke raya tattalin arzikinsu, shi ya sa, ba za a sa ran birnin Beijing ya kai ga ma'auni na Amurka ba. In an lura, a lokacin da Beijing ke fama da gurbacewar iska mai tsanani, , yawan kananan sinadaran da ke cikin iska ya kai sama da 800 ko 900, kuma dukkansu sun kai fiye da 60. Idan birnin Beijing ya iya cimma burin kamar yadda hukumar WHO ta tsara, to, za a ingancin iska zai samu kyautatuwa sosai a nan birnin, wato ke nan ya zuwa yanzu, akwai saura rina a kaba game da wannan aiki."
A cikin wani dogon lokaci, ana ganin cewa, motoci su ne babban dalilin gurbacewar iska. Mataimakin shugaban kwalejin nazarin harkokin kiyaye muhalli ta jami'ar Renmin Zou Ji ya bayyana cewa, ba sabo da karuwar yawan motocin da ake mallaka kawai ba, babban dalili shi ne yawan iska mai guba da motoci ke fitarwa a sanadin yadda ake yawan yin amfani da su, ya ce,"idan aka dauki biranen Beijing da New York a misali, za a gano cewa a birnin Beijing, akwai motoci da yawansu ya kai sama da miliyan 5, a birnin New York ma, akwai motoci kimanin miliyan 7. wato ke nan yawan motocin da ke birnin Beijing bai kai na birnin New York ba, amma, yawan motocin da ake yi amfani da su zuwa wurin aiki daga Litinin zuwa Jumma'a a birnin beijing ya fi na New York kwarai da gaske. Duk da cewa hanyoyin zirga-zirgar jama'a sun samu babban ci gaba a birnin Beijing, amma sabo da wasu dalilai, yawan mutanen da suke yi amfani da motocinsu na kansu zuwa aiki a Beijing ya fi na Tokyo da New York, sabo da haka ne, ake kara samun gurbatacciyar iska."
A cikin sabon shirin yaki da gurbatacewar iska da aka bayar, an tsara wasu matakai wajen hana gurbataccewar iska da motoci za su haifar, inda aka bayyana cewa, a manyan birane na kasar Sin kamar Beijing, Shanghai da Guangzhou, za a kuntata yawan motocin da ake amfani da su.
Bisa hasashen da aka yi, an ce, za a bukaci kudaden da yawansu ya kai biliyan 1750 wajen aiwatar da shirin yaki da gurbataccewar iska, abin kuma da za a sa kaimi ga karuwar aikin samar da kayayyaki wato GDP da kudin Sin yuan biliyan 2000. Mataimakin shugaban cibiyar nazarin kimiyyar kiyaye muhalli ta kasar Sin Chai Fahe ya ce, wannan matakin da kasar Sin za ta dauka zai yi amfani ga kyautata salon raya tattalin arzikin kasar Sin, ya ce,"Abin da ya fi muhimmanci shi ne daidaita salon samun bunkasuwa, da canja tsarin sana'o'i da daidaita tsarin yin amfani da makamashi, sabo da haka ne, bai kamata jama'a su mayar da shi tamkar wata manufar yaki da gurbacewar muhalli ba, a maimakon hakan, ya kamata a mayar da shi a matsayin wani muhimmin matakin da aka dauka na kyautata tsarin ci gaban zamantakewar al'umma da na tattalin arziki."(Bako)