A ranar Laraba 31 ga watan Oktoba, shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria, ya bayyana sauyawa wasu ministocin kasar biyu ma'aikatu. Ministocin da abin ya shafa su ne, na ma'aikatar makamashi Mr. Darius Dickson, da zai koma ma'aikatar lura da yankin Niger Delta a matsayin karamin minista, yayin da ita kuma karamar ministar ma'aikatar lura da yankin Niger Delta hajiya Zainab Ibrahim-Kuchi, za ta koma ma'aikatar makamashi a matsayin karamar minista. Shugaba Jonathan, ya bayyana wannan sauyi ne bayan taron mako-mako na majalisar zartaswar kasar da ya gabata a Larabar nan, haka nan sanarwar ta nuna cewa, sauyin zai fara aiki ne tun daga farkon mako mai zuwa.
A bakin mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman kan harkokin yada labaru Reuben Abati, wannan sauyi ba shi da wata nasaba da halin da wutar lantakin da kasar ke ciki, domin a cewarsa, yawan lantarkin da kasar ke samarwa na cigaba da karuwa, sama da yadda abin yake kafin tsohon ministan ma'aikatar farfesa Barth Nnaji, ya ajiye aikinsa a 'yan makwannin baya.(Saminu)