in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Jonathan na Najeriya zai kawo ziyarar aiki nan kasar Sin
2013-07-04 10:18:29 cri

Fadar shugaban kasa a Najeriya ta bayyana cewa, shugaba Goodluck Ebele Jonathan zai gudanar da wata ziyarar aiki ta kwanaki 5 a kasar Sin tun daga ranar Litinin mai zuwa. Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Reuben Abati ya sanyawa hannu ta ce, tawagar shugaban kasar za ta kunshi wasu gwamnoni, da ministoci da 'yan majalissar dokokin kasar, taren da wakilan sassa masu zaman kansu.

Ana sa ran shugaban kasar zai gana da shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da firimiya Li Keqiang, da kuma shugaban kwamitin majalisar wakilan jama'ar duk kasa Zhang Dejiang. Har ila yau, tattaunawa tsakanin shugabannin za ta hada da batutuwan da suka shafi hadin gwiwa a fannonin habaka hada-hadar albarkatun man fetir, da ababen more rayuwa, da samar da lantarki, noma, da harkar sadarwa da kuma batun yawan shakatawa.

Kafin kammalar wannan ziyara, ana sa ran rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da dama tsakanin bangarorin biyu. Bugu da kari, shugaba Jonathan zai halarci wani taron tattaunawa kan harkokin zuba jari tsakanin kasarsa da Sin, taron da zai samu halartar manyan 'yan kasuwar kasar ta Sin da kuma takwarorinsu na Nijeriya.

Bisa shirye-shiryen wannan ziyara, shugaban zai gana da jagororin manyan kamfanonin kasar Sin irinsu Huawei, da SINOPEC da kuma ZTE, zai kuma bude sabon ginin ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Sin, zai kuma aza harsashin ginin gidan jakadan Najeriyar a nan kasar Sin. Har ila yau, shugaban Najeriyar zai kai ziyara birnin Daqing dake arewa maso gabashin kasar Sin, inda zai ganewa idanunsa kamfanin sarrafa albarkatun mai, da gonakin gwaji na musamman, zai kuma gana da shuwagabannin yankin.

Shugaban kasar zai kuma gana da al'ummar Najeriya mazauna kasar Sin. Dangantaka tsakanin Najeriya da kasar Sin dai ta kasance mai dadadden tarihi, tana kuma gudana cikin nasara tun kafuwarta a shekarar 1971. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China