Kwanan baya a yayin da yake zantawa da manema labaru na kamfanin dillancin labaru na Xinhua, ministan harkokin waje da hadin kai na kasar Togo, Elliott Ohin ya nuna cewa, ana gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashen Togo da Sin ne bisa tushen nuna amincewa da juna, da girma juna, da kuma samun nasara tare, matakin da ya kai ga samun babbar nasara ta fuskar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Elliott Ohin ya bayyana cewa, a kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan girmama ikon mallakar kasashe abokanta a yayin da take bunkasa dangantakar dake tsakaninta da wadannan kasashe, ciki har da kasar Togo, kuma tana adawa da ayyukan kutsa kai cikin harkokin cikin gidansu da aka yi.
Kazalika Elliott Ohin ya nuna yabo sosai ga kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Togo, ya ce ana inganta dangantakar ne bisa amincewar juna, kuma ana iya shaida haka ta ayyukan hadin kai da dama da aka gudanar a tsakaninsu. Dukkansu sun taka muhimmiyar rawa wajen kyautata tattalin arziki da zaman rayuwar jama'ar kasar Togo, da kuma samar musu da guraban aikin yi.
A yayin da yake bayyana yadda kasashen biyu suka yi cudanya a shekaru sama da 40 da suka wuce, Olliott Ohin ya ce, a cikin wannan lokaci dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba cikin hanzari, kana a bangaren al'adu, cinikayya, kudi, ba da ilmi mai zurfi, kiwon lafiya, aikin gona, muhimman kayayyakin more rayuwa da sauransu, an samu cikakkiyar nasara.
Bayan haka kuma, Olliott Ohin ya bayyana cewa, kasar Sin ta soma aikin tura kungiyoyin masu aikin jinya zuwa kasar Togo a shekarar 1974, hidimar da suka samar ta samu yabo sosai daga kasar. A shekarar 1993, kasar Sin ta taimaka wajen gina wani asibiti dake da gadaje guda 100 a yankin Kara da ke kasar, wanda ya taimaka wajen kyautata na'urorin kiwon lafiya na Kara da kuma yankunan dake dab da wurin. A shekarar 2010, kasar Sin ta kara taimakawa wajen gina wani asibiti da wata cibiyar yaki da zazzabin cizon sauro a Lome, babban birnin kasar Togo. Bayan haka kuma, kasar Sin tana ba da tallafin magunguna da na'urorin aikin jinya ga asibitocin dake Kara da Lome a ko wace shekara, kana ta ba da kudin alawus, da kudin hidima, da kudin guraben kara samun ilmi ga daliban dake koyon ilmin likitanci a jami'o'in kasar Togo.
Kan batun nasarorin da kasashen biyu suka samu wajen hadin gwiwar aikin gona, Olliott Ohin ya bayyana cewa, kamfanin hadin gwiwar samar da sukari na Asnieres ya kasance wata babbar nasarar da aka samu ta fuskar hadin kan kasashen Sin da Togo. A yayin da kasar Sin ke kokarin ba da tallafin takin zamani da fasahohin aikin gona ga kasar Togo, a sa'i daya kuma ta taimaka wa kasar wajen kafa gonakan noman masara da shinkafa na gwaji masu inganci masu muraba'in ekoki 2 a arewacin kasar Togo, ta kuma kafa cibiyar gwada fasahohin aikin gona a kasar.
Bayan haka kuma, Olliott Ohin ya bayyana wa manema labaru kan nasarorin da kasashen Sin da Togo suka samu a fannonin aikin adana ruwa, ba da ilmi, al'adu, horar da kwararru, kudi, hanyoyin mota, da kuma gine-gine gwamnati, musamman ma babban dakin taro a karkashin taimakon kasar Sin da aka gina a yankin Kara, da filin wasa da fadar shugaban kasa a birnin Lome. Kana ya yi bayani kan wasu ayyukan hadin kai da yanzu haka ake yi, da kuma wadanda za a yi.
A karshe kuma, Olliott Ohin ya nuna yabo ga babbar nasara da kasar Sin ta samu wajen yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ya kuma bayyana fatansa na karfafa hadin gwiwa irin ta samun moriya tare da Sin a fannoni daban daban, domin taimaka wa kasar Togo ta fuskar tabbatar da ci gaban tattalin arziki. (Bilkisu)