Yanzu ana gudanar da aikin yadda ya kamata. Kwararrun kasar Sin a fannin gine-gine da ma'aikatan kasar Togo suna hada kansu sosai ba tare da wata matsala ba. Kuma ana sa ran cewa, nan da shekaru 2 masu zuwa za a kammala aikin kuma za a fara amfani da filin jiragen saman.
An labarta cewa, sabon bangaren tashi da saukar fasinja mai benaye 2 zai raba fasinjojin da suka sauka da wadanda suke shirin tashi. Sa'an nan kuma filin jiragen saman zai kara yawan fasinjojin da zai yi jigilarsu a ko wace shekara daga dubu 400 zuwa miliyan 2, kana kuma, zai kara yawan kayayyakin da zai yi jigilarsu a ko wace shekara daga ton dubu 10 zuwa ton dubu 50.




