Shugaba Hu Jintao ya bayyana cewa, a shekaru 40 da suka gabata, tsofaffin shugabannin kasashen biyu sun kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, wanda ya bude kafar sada zumunta a tsakanin kasashen biyu. A cikin shekaru 40 din, kasashen biyu sun sada zumunci, yin mu'amala bisa matsayin zaman daidai wa daida, yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, kana sun inganta dangantakarsu yadda ya kamata, wadda ta zama abin koyi ta fuskar hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Kasar Sin tana son yin amfani da damar cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Togo, don yin mu'amalar sada zumunta da fadada yin hadin gwiwa a tsakaninsu, a kokarin inganta dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi, kuma wannan zai taimakawa al'ummominsu.
Shugaba Faure ya ce, kasahen Togo da Sin sun fahimci juna ta fannin siyasa, da kuma samun moriyar juna a fannin tattalin arziki. A cikin shekaru 40 da suka wuce, bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa a fannonin aikin gona, ayyukan more rayuwa, kiwon lafiya, bada ilmi da dai sauransu, wanda ya kawo babbar moriya gare su. Kasar Togo tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen ci gaba da sa kaimi ga samun wadata da juna. (Zainab)




