in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya yi kira ga kungiyar G20 da ta dauki mataki don tinkarar hadarin hauhawar farashin abinci
2011-06-22 10:48:43 cri

A ran 21 ga wata, shugaban bankin duniya Robert B. Zoellick ya furta cewa, farashin abinci na duniya yana hawa da sauka fiye da kima, ya kamata kungiyar kasashen G20 ta dauki wani mataki domin taimakawa mutanen kasashe masu tasowa wajen tinkarar wannan matsala.

Mr. Zoellick ya bayar da wata sanarwa a wannan rana a bankin duniya cewa, hauhawar farashin abinci ko raguwarsa ya zama kalubale mafi tsanani a gaban mutanen kasashe masu tasowa, wanda ke kawo illa ga zaman rayuwar matalauta.

Mr. Zoellick ya jaddada cewa, a gun taron ministocin aikin gona na kungiyar G20 da aka yi a wannan mako a birnin Paris, taron ya yi kira ga ministocin aikin gona na kasashe daban daban da su yi hadin gwiwa domin tinkarar kalubalen hauhawar farashin abinci, da kafa tsarin bayar da labarun da suka shafi yawan abincin da aka adana.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China