in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hu Jintao ya gabatar da shawarwari a gun taron koli na kungiyar G20
2011-11-04 09:16:08 cri

An bude taron koli na kungiyar G20 karo na 6 a ran 3 ga wata a birnin Cannes na kasar Faransa. Inda shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi jawabi cewa, ya kamata kasashen kungiyar G20 su kara yin hadin gwiwa na kawo moriyar juna domin ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. Kana ya ba da shawara cewa, ya kamata kasashe daban daban su daidaita matsayinsu domin yin hadin gwiwa mai kawo moriyar juna da kyautata tsarin gudanarwa da neman samun bunkasuwa da kuma tabbatar da zaman wadata.

Bugu da kari, Hu Jintao ya nanata cewa, kasar Sin na son soke buga haraji da kashi 97 cikin dari na kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe marasa bunkasuwa wadanda suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin bisa tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. A cikin jawabinsa, ya gabatar da yanayin tattalin arzikin kasar Sin a takaice, kuma ya bayyana cewa, tun daga lokacin da rikicin hada-hadar kudi ya barke a duniya, kasar Sin ta yi ta kokarin raya tattalin arzikinta domin ba da gundummawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya, don haka ta kara zuba jari ga hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa da ba da taimako ga kasashe masu tasowa, ta yadda za ta ba da gundummawarta ga bunkasuwar wasu kasashen duniya a fannonin tattalin arziki da zaman al'umma da kyautata yanayin hada-hadar kudi na duniya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China