Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Afirka ta Kudu ta bayyana cewa, shugaban kasar Jacob Zuma zai halarci taron kungiyar kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki ko G20 a takaice, wanda ake fatan gudanarwa a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha, daga ranar Alhamis zuwa Juma'a mai zuwa.
Sanarwar da aka rabawa manema labarai a ranar Litinin, ta kara da cewa, taron kungiyar na wannan karo, ya zo a gabar da ake ci gaba da fama da matsalolin tattalin arzikin duniya, da tangal-tangal din kasuwannin hannayen jari ke yi, sakamakon rade-radin da ake yi cewa, Amurka na shirin janye kimanin dala miliyan dubu 85 da take zubawa a kasuwar a ko wane wata.
Har ila yau an bayyana cewa, shuwagabannin kasashe mambobin wannan kungiya za su tattauna kan batutuwan da suka shafi rashin daidaito, da halin rashin tabbas da kasashen duniya ke fuskanta a fannin farfadowar tattalin arzikinsu.
Sabili da haka dai gwamnatin Afrika ta Kudun na fatan wannan taro zai taimaka, wajen daidaita yanayin tattalin arzikin kasashen duniya baki daya, maimakon daukar matakan cimma moriyar daidaikun kasashe.
A cewar sanarwar, hakan na da fa'idar gaske, musamman a wannan gaba da kasashen India da Afirka ta Kudu ke nuna damuwa don gane da faduwar darajar kudadensu, lamarin da a bana kadai, ya kai ga karyewar darajar kudaden nasu da kaso 20 bisa dari. (Saminu)