A kwanaki 2 da suka gabata, Mista Baroin ya gana da Wang Qishan, mataimakin firaministan kasar Sin, da Xie Xuren, ministan kudi na kasar, gami da sauran wasu manyan jami'an Sin ta fuskar harkokin kudi, inda bangarorin 2 suka yi musayar ra'ayoyi kan yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki, batutuwan da za a tattauna a taron shugabannin G20 da zai gudana a watan Nuwamba, yadda za a gyara tsarin kudi na kasa da kasa, da rikicin bashi da kasashen Turai suke fama da shi. Ban da haka kuma, bangaren Faransa ya yi bayani filla-filla kan yadda kasashen Turai suke kokarin shawo kan matsalar tattalin arziki a kasar Girka. (Bello Wang)