in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ta Kudu zai kai ziyara Sudan ranar Talata
2013-09-02 10:02:28 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan SUNA, ya ba da rahoto a ranar Lahadi cewa, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit zai kai ziyara Khartoum, babban birnin kasar Sudan a ranar Talata, don tattaunawa da takwaransa na Sudan Omar al-Bashir game da batutuwan da kasashen biyu ke takaddama a kai.

A halin da ake ciki kuma, wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta bayar, ta bayyana fatan cewa, ziyarar shugaba Kiir za ta hanzarta aiwatar da yarjejeniyoyin hadin gwiwa tare da warware sauran batutuwan da ke tsakanin kasashen biyu, ta yadda zai taimaka wajen karfafa dangantaka da samar wa al'ummomin biyu zaman lafiya.

A cewar sanarwar, wadanda za su rufawa Kiir baya yayin ziyarar, sun hada da ministocin harkokin kasashen waje, dangantakar kasa da kasa, harkokin cikin gida, man fetur da hako ma'adinai, masana'antu da mataimakin ministan harkokin kudi, cinikayya da zuba jari da kuma wasu 'yan kasuwa.

Ana sa ran yayin ziyarar za a yi nazarin batutuwan da ba a warware ba tsakanin kasashen biyu, ciki har da batun yankin Abyei da batun mai, tsaro da kuma matsayin 'dan kasa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China