Sakamakon zabe da aka baiyana ranar Alhamis na nuna cewa, tsohon praministan kasar Mali, kuma tsohon shugaban majalisar kasar Ibrahim Boubarka Keita wanda akewa lakabi da IBK shi ne ya lashe zaben kasar ta yammacin Afirka.
IBK ya cimma nasarar samun kashi 77.61 a taki na biyu na zaben shugaban kasar da aka yi ran 11 ga watan Agusta, inda ya shige gaban abokin hamayyarsa Soumaila Cisse, mai shekaru 63 kuma tsohon ministan kudi wanda ya samu yawan kuri'u kashi 22.39 cikin dari.
Daga masu zabe 6,829,696 da akai wa rajista, kashi 45.78 ne suka yi zabe a taki na biyu.
A halin da ake ciki, magatakardan MDD Ban Ki-moon ya taya kasar Mali murna dangane da kare zaben shugaban kasar cikin nasara, inda ya jadadda cewar, MDD za ta ci gaba da goyon bayan kasar a fuskar gina zaman lafiya.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun MDD ya bayar, Mr. Ban ya taya Ibrahim Boubarka Keita murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar Mali, yayin da kasar ke jiran tabbatar da sakamakon daga kotun dokokin kasa. (Lami)