A ranar 6 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kammala ziyarar aiki a kasar Mexico, kuma ya tashi daga birnin Merida don ya kama hanyarsa ta zuwa jihar California da ke kasar Amurka, don ganawa da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama.
Kasar Mexico ta kasance zango na uku cikin ziyarar shugaban Xi a kasashe 4 na nahiyar Amurka. Tuni ya riga ya ziyarci kasashen Trinidad and Tobago da Costa Rica. An shirya shawarwari tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a ranar 7 da ranar 8 ga wata a gidan hutawa na Annenberg da ke jihar California, inda za su tattauna manyan batutuwan da suka dora muhimmanci sosai a kai da karfafa fahimtar juna, da ba da ra'ayoyinsu don kafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa da girmama juna da samun moriyar juna, kuma domin kafa sabon nau'in dangantakar da ke tsakanin manyan kasashe ta Sin da Amurka.(Bako)