Shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou ya sanya hannu a ranar Litinin kan wani kuduri dake ba da damar maye gurbin ministocin jam'iyyar Moden FA LUMANA da su ki shiga gwamnatin hadaka da aka kafa ranar 13 ga watan Agustan shekarar 2013.
Moden FA LUMANA ta shugaban majalisar dokokin kasar Nijar, Hama Amadou, dake kawance tare da jam'iyyar PNDS-TARAYYA mai mulki a kasar ta bayyana cewa, shugaban kasa bai shawarce ba wajen kafa wannan sabuwar gwamnatin hadaka. Bisa shawarar faraministan kasar Nijar Brigi Rafini ne shugaban kasar Nijar ya sanya hannu kan wannan kuduri dake kawo gyaran fuska kan kudurin ranar 13 ga watan Agusta na nada mambobin gwamnati. Bisa kudurin ne aka nada Amadou Boubacar Cisse ministan fasalin kasa, Asmane Abdou ministan ilimi mai zurfi, madam Yahaya Baare Haoua Abdou ministar yawon bude ido, madam Sani Mariama Moussa minister, wakiliya ta ministan kasa kuma ministan harkokin waje, madam Ibrahim Binta Fodi wakiliya ta ministan kasa kuma ministan fasalin kasa.
Sabuwar gwamnatin kasar Nijar na kunshe da mambobi 37 idan aka hada da faraminista. (Maman Ada)