in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar "Moulathamines" ta dauki alhakin kai hare-hare a Nijar
2013-07-09 11:00:51 cri

Kungiyar "Moulathamines" ta Moctar Belmoctar da aka fi sani da sunan Bellawar ta sanar a ranar Litinin da daukar alhakin kai hare-hare a biranen Yamai, Arlit da Agades na kasar Nijar, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na Nouakchott (ANI) ya bayar bisa amfani da wani sakon murya.

A yayin harin da aka kai kan gidan yarin birnin Yamai a cikin watan Yunin da ya gabata, fursunoni 30 suka tsere bayan da wasu mutane suka kai hari.

A cikin wannan sakon murya, kakakin kungiyar dake bayyana kansa a matsayin mamba na kungiyar ya ba da bayanai filla-filla, tare da jaddada cewa, sun fara shirya kai harin tun lokacin da suka kai harin hadin gwiwa tare da kungiyar Mujao a farkon watan Mayun da ya gabata kan rundunar sojojin kasar Nijar a Agades da kuma kamfanin Areva na kasar Faransa dake birnin Arlit.

Kakakin kungiyar ya nuna cewa, wannnan harin da aka kai a gidan yarin birnin Yamai a ranar daya ga watan Yuni da misalin karfe uku na yamma, agogon wurin da Abdalla Al Soudani ya jagoranta ya taimaka wajen murkushe jami'an tsaron gidan yarin na Yamai domin fitar da fursunoni kimanin talatin.

Da yake ba da karin haske kan harin Agades da Arlit, ya bayyana cewa, kusan sojoji 116 da suka hada ofisoshi da masu horar da sojoji na kasar Faransa suka kashe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China