Wannan rahoto ya kasance rahoton farko da hukumar cinikayya ta kasar Sin ta bayar dangane da dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da Afrika, wanda ya waiwayin ci gaban dangantakar bangarorin biyu a cikin shekaru 60 da suka gabata, kuma ya yi tsinkaye kan ci gaban da za su samu wajen hadin kai ta fuskar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.
A gun bikin gabatar da rahoton, jakadan kasar Sin dake kasar Uganda Sun Heping ya ce, dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare a fuskar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da Afrika ba ma kawai za ta yi amfani ga bangarorin biyu ba, har ma za ta kawo tasiri ga zaman lafiya, karko da bunkasuwar duniya.(Amina)