in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwwar cinikayya da tattalin arziki da ke tsakanin Sin da Africa na da muhimmanci, a cewar AFDB
2011-10-28 13:46:58 cri

An lura cewa huldar cinikayya tsakanin Sin da Africa yana cigaba sosai kuma Sin abokiyar hulda ce mai kyau ta fannin tattalin arziki.

Mthuli Ncube, mataimakin shugaban Bankin raya kasahen Africa, wato AFDB wanda kuma shi ne babban jami'i a fannin tattalin arziki, a hira ta musamman da ya yi da kamfanin dillancin labaru ta kasar Sin Xinhua, Alhamis din nan a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. Ya ce Sin tana da dangantaka mai karfi da Africa a halin yanzu kuma dangantakar na kara karfi ko wace shekara.

Mr. Ncube ya kuma ce, Sin tana cike gurbi a fannin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a Africa ta hanyar zuba jari sosai a nahiyar baki daya.

Bankin AFDB ya kaddamar da wani littafi a watan jiya akan dangantakar dake tsakanin Sin da Africa, Ncube ya ce littafin ya mai da hankali ne kan hakikanin hanyoyin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Africa.

Ya lura da cewa Sin tana ta kafa masana'antu da cibiyoyin tattalin arziki a kasashen Africa, hakan aka samar da guraban aikin yi ga mazauna wurin.

Ana gudanar da taron tattalin arziki kashi na 6 a cibiyar tattalin arzikin kasashen Africa ta MDD wato UN-ECA dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha, wanda aka mai taken 'tattalin arzikin da ake samu daga amfanin gona da kuma shirin aiwatar da sauye-sauye a Africa".

Game da taron kuma Ncube ya kara da cewa, akwai kafofi da yawa ma Sin da za ta zuba jari ta fannin bunkasa manyan kayayyakin more rayuwa ta hanyar tsimin makamashi a nahiyar Africa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China