in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne mizanin harkokin cinikayyar dake tsakanin Sin da nahiyar Afrika ya kara daukaka sosai a 2011
2011-12-05 15:58:29 cri

A ranar larabar da ta gabata wani babban Jami`i a ma`aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya ce akwai alamun dake nuna cewa harkokin ciniki da ke tsakanin kasar Sin da kasashen dake nahiyar Afrika a 2011 zai kai wani sabon matsayin tarihi.

Mr. Shen Danyang mai magana da yawun ma`aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya fada yayin wani taron manema labarai cewa adadin cinikayyar kasashen yana karuwa da kashi 30 a kowace shekara, wanda a kididdigar da aka yi a 2011 adadin cinikin ya kai dalar Amurka biliyan 122.2 a farkon watanni tara na 2011 idan aka kwatanta da biliyan 126.9 da aka samu a shekarar bara.

Jami`in ya cigaba da cewa yanzu kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikin kasashen Afrika a yayin da harkokin ciniki na karuwa da kashi 28 cikin dari a kowace shekara cikin a tsawon shekaru 10.

Ya zuwa karshen shekarar 2010, sama da kamfanonin kasar Sin 2,000 ne suka saka jarinsu a nahiyar ta Afrika, ko a cikin watanni tara na farkon 2011, kasar Sin ta saka jarin da ya kai dalar amurka biliyan 1.08 a bangarorin da ba su shafi kudade ba dake nahiyar.

Mr. Shen Danyang ya ce hakika dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ta fuskar sha`anin sadarwa da yawon bude idanu ta kai wani muhimmin matsayi, domin da yawa daga cikin cibiyoyin hada-hadar kudade na kasar Sin suna gudanar da harkokinsu a nahiyar Afrika, kuma a yanzu haka kamfanonin sufurin jiragen sama na kasar Sin sun bude kofar zirga-zirga ta kai tsaya zuwa nahiyar.(BAGWAI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China