Wani mai kula da harkokin ciniki na ma'aikatar harkokin kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan, dangantakar cinikayya dake tsakanin kasashen Sin da Afirka ya bunkasa a cikin sauri a fannoni daban daban, kuma ta zama abokiyar hadin gwiwa a duk fannoni wadda ke da muhimmanci ga bunkasuwar al'ummomin da tattalin arziki na bangarorin biyu. Kasar Sin ita ce sahihiyar aminiya ta Afirka, za ta yi musayar ra'ayoyi kan harkokin bunkasuwa tare da kasashen bisa ka'idojin na zaman daidaici da moriyar juna da neman bunkasa tare. Bugu da kari, kasar Sin ta nuna goyon baya da taimako ga kasashen Afirka ta hanyar zuba jari da ba da gudumawa, don tabbatar da moriyar juna da samun bunkasawa tare a tsakaninsu. (Zainab Zhu)