Rahotanni daga Bagadaza, babban birnin kasar Iraki na nuna cewa, sakamakon sabbin hare-hare na bindigogi da bama-bamai na baya bayan nan a ranar Laraban nan, akalla mutane 57 ne suka halaka, kusan 207 kuma suka ji rauni a cikin watan dayan nan da irin wannan al'amari ke ta faruwa.
Ya zuwa yanzu dai, babu wata kungiya da ta sanar da daukan nauyin aikata wannan ta'adda, sai dai kungiyar Al-Qaida tana sahun gaba a irin wadannan hare-hare, yawancin abin da ke kara kawo fargaban cewa, kungiyar ta'addancin da sauran kungiyoyin masu nau'i daya na kara kai hare-haren tashin hankali, musamman ma ganin kasar tana kokarin hana yaduwar rikicin da ake yi a makwabciyar ta kasar Sham.
Wannan harin dai ya zo ne bayan da firaministan kasar Nuri Al-Maliki ya sanar a ranar Laraban cewa, ana zaman sauraren yiwuwar kai hari a kasar Sham da ke makwabtaka da ita, yana mai bayanin cewa, wannan harin zai iya shafar kasar da suke makwabtaka da juna ta hanyar tattalin arzikinta da ayyukan jama'a.
Wannan sanarwa ta Maliki ta zo ne lokacin da kasashen yammaci ke shirin amfani da wani dalilin da zai sa su kai ma Sham hari na soja sakamakon zargin da ake mata cewa, ta yi amfani da makamai masu guba a wassu wurare a Damascus wajen fada da 'yan adawa, abin da ya salwantar da rayukan fararen hula da yawa. (Fatimah)