in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 18 sun mutu a wasu sabbin hare-hare a kasar Iraki
2013-08-26 14:27:21 cri

A ranar Lahadi da yamma, an samu fashewar wasu bama bamai da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha takwas tare da jikkata wasu kusan sittin a gundumar Diyala dake gabashin kasar Iraki, da kuma Bagadaza, babban birnin kasar, a wani labarin da kamfanin dillancin labara kasar Sin Xinhua ya samu daga wasu majiyoyi masu tushe.

Hari mafi muni ya abku a yayin da wani bam da aka dana a cikin wata motar ya tashi a wata kasuwar dake Baqouba a gundumar Diyala dake fama da tashe tashen hankali mai tazarar kilomita 65 daga arewa maso gabashin birnin Bagadaza, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 13 da jikkata wasu 36, in ji magajin garin Baqouba, Albdullahi al-Haiyali a cikin wata hirarsa da Xinhua. A cikin wani harin kuma, farar hula guda ne ya mutu a yayin da goma suka ji rauni bayan da wata nikiya ta fashe a kan hanyar da ke kusa da wani gida a arewa maso gabashin karkarar Baqouba, a cewar hukumonin 'yan sandar wurin. A birnin Bagadaza kuma mutane biyu suka rasa rayukansu a yayin da bam ya tashi a cikin wata mota da raunana wasu mutane bakwai, duk dai a cikin wannan hari na unguwar Zaiyouna, a cewar wata majiya mai tushe daga ma'aikatar harkoki cikin gida da ta nemi a sakaya sunanta. Haka kuma an samu tashin bam a kan wata hanyar dake unguwar Shaab a arewa maso gabashin Bagadaza wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da raunana mutane takwas, a cewar wannan majiya. Kasar Iraki da dai na fama da tashe tashen hankali da ake fargabar sake janyo tashen tashen hankali irin na yake yaken basasar da suka barke a shekarar 2006 da kuma shekarar 2007 da suka haddasa mutuwar adadin mutane a ko wane wata ya rika wuce dubu uku. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China