in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da ke zaune a garuruwa da birane na kasar Sin zai kai kashi 70 cikin 100 a shekarar 2030
2013-08-28 14:03:21 cri
A ranar 27 ga wata, a nan birnin Beijing, hukumar kula da tsara shirin samun bunkasuwa ta M.D.D. wato UNDP ta bayar da rahoton raya dan Adam na kasar Sin na shekarar 2013, inda ta yi hasashe cewa, ya zuwa shekarar 2030, za a kara samun mazaunan birane da yawansu zai kai miliyan 310, kuma yawan mutanen da ke zaune a garuruwa da birane na kasar Sin zai kai kashi 70 cikin 100. Ya zuwa wancan lokaci, yawan mutanen da ke zaune a birane zai zarce biliyan 1.

A cikin rahoton, an bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun nan, bayan karfafa yunkurin raya birane da garuruwa na kasar Sin, yawan mutanen da ke zaune a birane ya karu daga kashi 13 cikin 100 na shekarar 1950, har zuwa yanzu, wato wannan adadi ya kai kashi 52.6 cikin 100 a shekarar 2012. A cikin shekaru 20 da suka gabata, yunkurin raya birane ya zama babbar hujjar da aka samu bunkasuwar tattalin arziki a kasar Sin, kuma an yi hasashe cewa, nan gaba, za a ci gaba da karfafa wannan yunkuri cikin shekaru goma-gomai masu zuwa.

A gun taron manema labaru game da fidda wannan rahoto, mataimakiyar sakatare janar na M.D.D. kuma shugabar hukumar UNDP Helen Clark ta bayyana cewa, yanzu, kasar Sin tana gaggauta yunkurin raya birane da garurruwa da ba a taba ganin irinsa ba, cikin tarihi. Ta ce, a cikin shekaru 60 ne kawai, kasar Sin ta cimma burin kara yawan mutanen da suka zaune a birane da garurruwa daga kashi 10 cikin 100 zuwa kashi 50 cikin 100, amma kuma kasashen Turai sun shafe shekaru 150 don cimma wannan buri, har ma da kasashen Latin Amurka duk, sun dauki shekaru 210 don samun wannan ci gaba.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China