Wani sojin kasar Afrika ta Kudu ya jikkata a cikin wani harin 'yan tawaye a jamhuriyyar demokaradiyyar Congo DRC, a wani labari na ranar Lahadi da kafofin kasar Afrika ta Kudu suka bayar.
A cewar tawayar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar DRC, sojin Afrika ta Kudu da wasu sojojin kasar Tanzaniya sun ji rauni a yayin wani harin 'yan kasar Congo kusa da birnin Goma dake gabashin wannan kasa.
A ranar Asabar dai ne, sojojin Afrika ta Kudu suka karyata wani labarin kafofin watsa labarai da bayyana cewa, sojojin MDD sun yi bata kashi da 'yan tawayen Congo.
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya sanar da majalisar dokokin kasarsa a ranar Jumma'a kan tura sojojin kasar fiye da 1300 a kasar DRC, a cikin rundunar sojojin MDD wadda wa'adinta ya fara daga ranar 13 ga watan Yunin shekarar 2013 zuwa ranar 31 ga Maris na shekarar 2014. (Maman Ada)