Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, ko MONUSCO a takaice, na kara kaimi wajen gudanar da sintiri a gabashin kasar, sakamakon karin fadace-fadace dake barkewa tsakanin sassan mayakan sa kai dake yankin.
Da yake tabbatar da daukar wannan mataki ga manema labarai, mataimakin kakakin MDD Eduardo del Buey, ya ce, ko da a ranar Litinin din da ta gabata, sai da wasu mayaka dauke da makamai suka yi musayar wuta a Pinga, dake lardin arewacin Kivu, kusa da sansanin MONUSCO dake yankin. Wannan dauki ba dadi da mayakan suka yi dai ya dace da lokacin ziyarar farko da sabon wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar Martin Kobler ya gudanar.
Cikin matakan da tawagar ke dauka na ba da kariya ga fararen hula, da kuma ragowar ma'aikatanta, a cewar del Buey, an girke jami'an tsaro kimanin 1,000 a sansanin dake Pinga, baya ga sintiri da jirage masu saukar ungulu dauke da jami'an tsaro ke yi a yankin. (Saminu)