in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da kamfen wayar kan jama'a a Burundi domin karbe makamai daga fararen hula
2013-05-28 11:02:03 cri

Tun bayan kamfen wayar da kan jama'a na farko na karbe makamai daga fararen hula da ya gudana daga ranar 19 zuwa 28 ga watan Oktoban shekarar 2009, kwamitin kasa mai daukan nauyin karbe makamai daga fararen hula a kasar Burundi, ya bayyana a ranar Litinin cewa, za'a shirya kaddamar da irin wannan yakin fadakarwa karo na biyu a ranar Talata bisa batun karbe makamai daga hannun fararen hula.

Bayan kudurin watan Janairun shekarar 2013 na dokar da ta shafi kananan makamai da makamantansu, yanzu ana kan shirin gudanar da wani kamfen wayar da jama'a na biyu kuma matakin farko zai fara daga ranar 28 ga watan Mayun shekarar 2013 tare da bikin kadammarwa da tarurukan shirye-shirye zuwa ga dukkan masu ruwa da tsaki da za su halarci wannan kamfe na biyu, in ji mista Zenon Ndabaneze, shugaban wannan kwamiti.

Haka kuma mista Ndabaneze ya jaddada cewa, a yayin kamfen wayar da jama'a na farko a shekarar 2009, makamai da dama ne da matune suka mika bisa radin kansu, suka hada da gurmeti dubu goma sha shida, bindigogi iri daban daban fiye da dubu biyu da dari bakwai, da kuma harsasai fiye da dubu dari da satin da nakiyoyi fiye da dubu biyar.

Kasar Burundi ta yi fama a shekaru da yake-yake basasa, wadanda suka tura mutanen kasar sayan makamai daga hukumomin kasar domin kare kansu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China