Ministan tsaron kasar Burundi Gabriel Nizigama ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ran Litini cewar, za'a tura rukunin farko na dakarun 'yan sandan kasar Burundi da yawansu ya kai a kalla 200 zuwa aikin kawo zaman lafiya a kasar Somalia nan da karshen wannan shekara.
Ya ce, wannan shi ne rukunin farko na dakarun 'yan sanda da za'a tura Somalia kuma za'a zabo su ne daga fannoni 3 na hukumar 'yan sandan.
Ministan tsaron ya kara da cewa, ana kan yiwa 'yan sandan gwaji har ma da gwajin ilmin ingancin lafiya, don zabo mafi dacewa da za'a tura aikin kawo zaman lafiya a Somalia.
Mr. Gabriel Nizigama ya ce, bayan an gama zabo su, za'a ba su horo na musamman kan aikin kawo zaman lafiya bisa tanadin MDD.
Ban da shirin horon, ministan ya ce, jami'an na bukatar kayan aiki na musamman.
Koda yake ya ce, bai san daidai lokacin da za'a tura dakarun Somalia ba, tana yiwuwa a karshen shekarar nan ne, wato bayan an kawo masu kayan aikin.
Kasar Burundi na cikin kasashe da ke ba da gudummawar dakaru ga shirin aikin kawo zaman lafiya a kasar Somalia, wato AMISOM inda zuwa yanzu ta tura bataliyar dakaru guda 6 tun shekarar 2007 don maido da zaman lafiya da tsaro a yankin.(Lami)