A ranar Litinin 6 ga watan nan ne shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza, ya yi wata ganawa da tawagar wasu jami'an kasar Sin a fadarsa, ziyarar da ta baiwa bangarorin biyu zarafin tattauna batutuwan da suka shafi daukaka dangantakar kasashen biyu zuwa matsayi na gaba.
Tawagar jami'an kasar ta Sin dai ta samu jagorancin shugaban kungiyar abokantakar Sin da kasashen Afirka Abdul'ahat Abdurixit. Har ila yau tawagar ta gana da mataimakin shugaban kasar Therence Sinunguruza a ranar Lahadin da ta gabata.
A cewar mataimakin kakakin fadar gwamnatin Burundin Willy Nyamitwe, Sin da kasar Burundi na da kyakkyawar alaka ta tsahon lokaci, kuma a wannan karo, tawagar ta kungiyar abokantakar Sin da kasashen Afirka CAPFA ko a takaice, ta ziyarci Burundin ne, domin ganin yanayin da ayyukan tallafi da Sin ke gudanarwa a kasar ke wakana. Nyamitwe ya ce, wakilan tawagar ta Sin sun gamsu da irin ci gaban da suka ganewa idanunsu.
Bugu da kari, wakilan sun bukaci dorewar dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. har wa yau a tabakin mataimakin kakakin fadar gwamnatin Burundin, kasar Sin na bayyana aniyarta, a fagen tallafawa ayyukan ilimi, a sashen horas da malaman makarantu na ENS dake jami'ar Burundi.
Kasar Burundi dai ta jima tana samun tallafi daka Sin, musamman a fannonin bunkasa ilimi, da lafiya, da sashen makamashi, da kuma samar da ababen more rayuwa.(Saminu)