Kasar Burundi za ta ci gajiyar shirin tallafin MDD na UNDAF, wanda zai taimaka wajen bunkasa bin doka da oda a kasar, da daidaita tsakanin jinsuna, da kuma inganta fannin tattalin arziki, shirin da ake fatan zai gudana daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2016.
Gwamnatin kasar ta Burundi ce dai ta tabbatar da wannan batu, bayan da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakaninta da MDD, wadda kuma ake sa ran za ta lashe dalar Amurka miliyan 600.
Wannan dai tallafin da kasar ta Burundi da ke gabashin nahiyar Afirka ta samu, ya biyo bayan taron nemawa kasar taimako, da ya gabata a birnin Geneva cikin watan Octobar shekarar da ta shude, wanda ke da nufin ba ta damar cimma burikan ci gaban ta masu lakabin PRSP kashi na biyu.(Saminu)