in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Samar da kyakkyawan tsari mai dorewa hanyar ci gaba ce a Somaliya, in ji jami'in MDD
2013-08-27 10:24:20 cri

Wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar Somaliya Nicholas Kay, ya jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da kyawawan shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya, a matsayin hanya daya tilo ta samar da ci gaba a kasar, duk kuwa da tarin kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu.

Mai magana da yawun MDD Farhan Haq ne ya rawaito Kay, na wannan tsokaci, yayin taron ganawa da manema labaru na rana rana da ake gudanarwa. Haq, ya kuma rawaito wakilin musamman na babban magatakardar MDD a Somaliyan na bayyana irin ci gaban da gwamnatin kasar ta samu tsakanin shekara guda da ta yi da kafuwa. Yayin jawabinsa gaban mahalarta taron kungiyar AU, Kay, ya yi imanin samun yanayi na koma baya, muddin dai ba a tabbatar da dorewar shirye-shiryen da ake gudanarwa a halin yanzu ba.

Kay, wanda ke jagorantar rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta UNSOM, ya kara da cewa, kawo yanzu kasar na fuskantar kalubale da dama, ciki hadda batun tsanantar yanayin tsaro a kudancin kasar.

Sakamakon hakan ne ma ya sa, a cewarsa, tawagar ta UNSOM ta lashi takobin ci gaba da marawa gwamnatin tarayyar kasar baya, a fagen inganta tsarin siyasar kasar, da tabbatar da samar da yanayin gudanarwa mai nagarta, tare da wanzar da doka da oda a dukkanin sassan kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China