Bisa rahoton da hukumar harkokin jama'a ta lardin Guangdong ta bayar, an ce, a sakamakon mahaukaciyar guguwa ta Utor, mafi yawan yankunan wannan lardi suna fama da bala'un ruwan sama kamar da bakin kwarya, da ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa daga tsaunuka da sauransu, wadanda suka yi illa ga rayuwar jama'a miliyan 4.16 daga birane 18, a cikinsu kuma mutane 20 sun mutu yayin da wasu 7 suka bace.
An tsugunar da mutane dubu 513 cikin gaggawa. Gidaje dubu 26 sun lalace. Jimillar hasarar kai tsaye dai ta kai yuan biliyan 4.9.
Kawon yanzu, hukumar harkokin jama'a ta lardin Guangdong ta riga ta dauki matakan aikin ceto bisa mataki na biyu, kuma ta tura wani rukunin aiki domin yin bincike kan yanayin da ake ciki, tare da kebe kayayyakin agaji, domin tsugunar da masu fama da bala'in yadda ya kamata.(Fatima)