Sanarwar ta ce, a ganin mahalartan taro, gwamnatocin kasashe daban-daban suna ba da babban taimako wajen sarrafa albarkatun ruwa, hakan ya sa, an yi kira ga kasashen dake mallakar mafarin ruwa gaba daya da su kara hadin kai da tuntubar juna bisa dokar kasa da kasa ta yadda za su ingiza bunkasuwar kasa da kasa.
Haka zalika sanarwar ta yi kira ga kasashen dake mallakar mafarin ruwa gaba daya su sarrafa wadannan matattarun ruwa ta yadda za su kasance wani tushe ga ayyuka da dama da wadannan kasashe za su amfana a nan gaba, ciki hadda samun bunkasuwa mai dorewa, kawar da talauci da yunwa, tabbatar da isashen hatsi, tinkarar sauyin yanayi, kiyaye muhalli, yin rigakafin bala'u daga indallahi, da kuma tabbatar da bunkasuwar birane da kauyuka cikin dogon lokaci har ma da kiyaye zaman lafiya da samun bunkasuwa. Mahalartan taron sun yi alkawarin cewa, za su mai da albarkatun ruwa a matsayin wani mataki ne da aka dauka domin kiyaye amincewar juna da hadin gwiwa tsakanin kasashe daban-daban da kuma raya kasashensu gaba daya. (Amina)