in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD na gudanar da sintiri a Sudan ta Kudu
2013-08-21 14:17:00 cri

A yunkurinta na sake dawo da kyakkyawan yanayin zaman lafiya da tsaro a gundumar Pibor, dake kasar Sudan ta Kudu, tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ko UNMISS a takaice, ta fara gudanar da wani sintiri na rana rana a wannan yanki, wanda a baya ya sha fama da rikice-rikice da tashe-tashen hankula da dama.

Kakakin babban magatakardar MDD Martin Nesirky ne ya bayyana hakan ga manema labaru a ranar Talata. Nesirky ya ce, burin tawagar ta UNMISS ne ta ga ta kare fararen hula daga dukkanin barazanar mahara, tare da samar musu damar zirga-zirga a wuraren da za su samu tallafi na ababen bukatun yau da kullum.

A cewarsa, sintirin da aka fara gudanarwa, na samun tallafi daga dukkanin jami'an tsaron yankin, kuma tawagar MDD na kokarin gano mutanen da suka tsere daga gidajensu, sakamakon fadace-fadacen da suka addabi yankin na Pibor, da Gumuruk, da ma ragowar sassan da ke fama da matsalolin tsaro. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China