in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin kan al'ummar Cote d'Ivoire shi ne ginshikin zaman lafiya, in ji MDD
2013-08-20 10:44:28 cri

Babban mai sa ido kan harkokin jin kai na MDD a kasar Cote d'Ivoire, Ndolamb Ngokwey ya bayyana a ranar Litinin a birnin Abidjan cewa, hadin kan al'ummar kasar Cote d'Ivoire shi ne babban ginshikin tabbatar da zaman lafiya a wannan kasar bayan ta kwashe shekaru da dama tana fuskantar rikicin siyasa da na sojoji wanda ya rika janyo tashen tashen hankalin dake da nasaba da zabubuka da suka yi sanadiyyar mutane akalla dubu uku a shekarar 2010 zuwa 2011. Bayan wannan lokaci na rikici da ya janyo rabuwar kawunan jama'a, hadin kan al'umma babban ginshiki ne da zai taimaka wajen kawo wani sabon yunkuri na tabbatar da zaman jituwa, sasantawa da zaman lafiya, in ji mista Ndolamb Ngokwy a yayin bikin kasa na ranar taimakon jin kai ta duniya. A kasar Cote d'Ivoire, an gudanar da bikin wannan rana bisa taken "duniya na bukatar hadin kan al'umma a wannan zamani."

A cewar cibiyar kula da harkokin ayyukan jin kai ta majalisar dinkin duniya (OCHA), matsalar jin kai ta kyautatu tun bayan rikicin siyasa na shekarar 2010 zuwa ta 2011 wanda ya janyo hijirar mutanen kasar dubu dari biyu da hamshin zuwa kasashen dake makwabtaka da Cote d'Ivoire a yayin da rikicin ya tsananta.

Kashi 91 cikin 100 na 'yan gudun hijira na cikin gida. kuma kashi 70 cikin 100 na wadanda suka fice daga kasar sun dawo gidanjensu, in ji OCHA tare da kara bayyana cewa, sakamakon wannan rikici har yanzu ana jin shi ta fuskar matsalar karancin abinci mai gina jiki, tsaro da hidimar zaman al'umma mai tushe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China